Saturday, 29 July 2017

Abubuwa masu birgewa kan Yanda ayyukan halittar jikin mutum ke gudana

Allah ya halicci jikin mutum ta yanda yana yin ayyuka daban-daban masu ban sha'awa da ban mamaki, masana sunyi kokarin fahim tar ainihin yanda halittar jikin dan adam take da yanda take aiki, ga kadan daga cikin abinda suka fahimta na gudanarwar jikin dan adam.

Kwayoyin halitta guda octillion bakwaine suke hade a jikin cikakken mutum(baka san ko nawane ake kira da octillion ba?danna nan domin sani).

Mutane na shafe shekaru biyar suna cin abinci(wannan yana nufin idan aka hade lokutan da mutum ke zama yana cin abincine tun daga farko har zuwa karshen rayuwarshi).

Cikakken mutum yakan bata kashi talatin da uku cikin dari na rayuwarshi yana bacci(wannan yana nufin idan aka hade lokutan da mutum yayi yana baccine tun daga farkon lokacin daya zama cikakken mutum har zuwa karshen rayuwarshi).

A cikin halittun Duniya, mutum ne kawai ke Iya yin bacci a kan gadon bayanshi.

Zuciyar mutumin da yayi matsakaiciyar rayuwa, zata buga sau biliyan uku a tsawon rayuwarshi.Farce yafi saurin fitowa a yatsun da kake amfani dasu wajen yin rubutu, haka kuma farce yafi saurin fitowa a yatsun da sukafi tsawo, kuma dai farcen yatsun hannu yafi na yatsun kafa saurin fitowa, sau kusan linki hudu.

Bazaka iyayin atishawa ba idanunka a bude.

Irin kwayoyin halittar fata dake bakin mutumne ke a farjin mace.

Hanci da kunnen mutum kullun kara girma suke har ya mutu, amma idan mutum baya kara girma, tun daga haihuwa har mutuwa.

Cikakken mutum bazai iya hadiye yawuba da yin numfashi a lokaci gudaba, amma jariri yana iyayin haka, har na tsawon watanni bakwai.

Zuciyar mata tafi ta maza saurin bugawa(buga jini a cikin jiki).

An taba samun wani mutum me suna Charles Osborne daya shafe shafe shekaru sittin da takwas yana ta shakuwa.

Mafi yawancin mutane basa iya bayar da labarin yawancin mafarkin da sukayi bayan sun tashi bacci, saboda sun manta.

Bacci na sace yawancin mutane cikin mintuna bakwai da niyyar yinshi.

Yawancin mutane masu amfani da hannun dama suna amfani da bangaren bakinsu na damane wajen tauna abinci, haka kuma yawancin mutane dake amfani da hannun hagu sun amfani da bangaren bakinsu na hagune wajen tauna abinci.

Kashi bakwaine kacal na mutanen Duniya ke amfani da hannun hagu wajen gudanar da al'amuransu.

Maza sunfi mata yawan kifta ido, kusan sau linki biyu.

Cikakken mutum na shaka da fitar da lumfashi sau dubu ashirin da uku a rana.

A lokacin da aka haifi mutum, akwai kwayoyin halitta guda biliyan goma sha hudu a cikin kwakwalwarshi,  kuma wannan yawan kwayoyin halitta bazai karuba har mutun ya mutu, a lokacin da mutum yakai shekaru ashirin da biyar, kwayoyin halittar kwakwalwar tashi guda dubu dari zasu rika raguwa a kullun, a lokacin da mutum yakai shekaru arba'in, raguwar yawan kwayoyin halittar dake cikin kwakwalwarshi zai karu sosai, a shekaru hamsin kuwa, kwayoyin halittar sunyi raguwar da har sai kwakwalwar mutum ta rage girma.

A lokacin da aka haifi mutum, akwai kasusuwa guda dari uku a jikinshi, amma da yakailokacin daya zama cikakken mutum, kasusuwan na raguwa zuwa dari biyu da shida.

A duk shekara, fiye da mutane miliyan biyu masu amfani da hannun hagu suna mutuwa, saboda kuskuren da sukeyi wajen aiki da na'urorin da akayisu damin mutane masu amfani da hannun dama.

Rashin samun bacci yafi rashin cin abinci matsala, saboda rashin samun bacci yafi saurin kashe mutum da wuri fiye da rashin cin abinci, ittifakin likitoci ya nuna cewa idan mutum ya kwana goma baiyi bacciba kwata-kwata da wuya bai mutuba, amma mutum zai iya daukar makwanni ba tare dayaci abinciba kuma yaci gaba da rayuwa.

Wani bincike da kwararrun bincike na kasar Jamus sukayi ya nuna cewa anfi samun cutar bugawar zuciya Ranar litinin fiye da ko wace rana a cikin mako.

Tsawon mutum na raguwa kadan da yamma.

A kalla, matsakaicin mutum na fadin kalmomi fiye da dubu hudu a duk rana.

Kididdiga ta nuna cewa a cikin mutane biliyan biyu, mutum dayane kawai ke kai shekaru dari da shashida a Duniya kamin ya mutu.

Yanda gashin mutum ke tsorowa yana nin kawa sau biyu idan yana tafiya a jirgin sama.


No comments:

Post a Comment