Monday, 31 July 2017

Al'adar tono gawa daga kabari a yimata kwalliya

Wannan hoton wasu matattune da danginsu suka cirosu daga kaburburansu suka kakkabe musu kurar dake jikinsu suka kuma canja musu kayan.

Wata kabilace a kasar Indonesiya keda irin wannan al'ada, wadda wai nuna soyayyace ga mamaci, bayan rasuwarshi da wani dan lokaci, danginshi zasuje su tonoshi daga kabari, sukakkabemai jiki, sannan su sakamai sabbin kaya, sannan a shanya gawar a cikin rana.

Wannan ma wata yarinyace wadda ta rasu, amma aka saka mata kayan sawa masu kyau, kannenta suka zauna a kusa da ita suna nunamata kayan wasanni na yara, kamar dai da ranta, wannan irin al'ada tana da ban mamaki.Lalla wannan shine Allah daya gari banban
National geography.

No comments:

Post a Comment