Thursday, 20 July 2017

An dakatar da fitar da shirin fim din da aka kwaikwayi Boko Haram a cikinshi

An dakatar da wani shirin fim da akayi niyyar fitarwa wanda aka kwaikwayi mayakan BoKo Haram a cikinshi, fim din me suna Aliko wanda kamfanin UK Entertaiment yayi niyyar fitarwa ya kwaikwayi shugaban kungiyar BoKo Haram(Shekau), amma daga baya wadanda suka shirya fim din  sunce bayan tattaunawa da shawarwari da masana da sukayi, sun fasa fitar da fim din har sai mama ta gani(babu rana).

Mutane sun mayar da martani akan wannan shawara ta dakatar da shirin Aliko, inda wasu sukace, ai abinda ya wucene ake yin fim akanshi saboda tarihi da kuma nunawa wadanda basu riski lokacin ba yanda abin ya kasance, sannan waau sukace ai masu shirin fim din sunji tsorone, wasu kuwa cewa sukayi wai basira ko kuma labarai sun karewa masu shirya fim dinne da sai sunyi fim akan Boko Haram?.

No comments:

Post a Comment