Saturday, 15 July 2017

An daura auren Nazir Ahmad tare da amaryarshi Halima

Shahararren mawakin hausa, Nazir Ahmad ya auri masoyiyarahi Halima a ranar Juma'arnan data gabata, kuma wani abin birgewa da auren Nazir da amaryarshi Halimatu Shine basuyi irin hotunan nan na zamani da akeyi kamin bikiba wanda zakaga amarya da ango kamin daurin aure anyi hotuna kala-kala anata watsawa, koda dai sunyi irin wadannan to ba'su watsasuba.

Nazifi Asnanic, Ali Jita, da Aminu Saira na daga cikin wadanda suka samu halartar wurin wannan daurin aure, muna musu fatan Allah ya bada zaman lafiya ya kuma kawo zuri'a ta gari. Amin.

Karin hotuna.


No comments:

Post a Comment