Thursday, 27 July 2017

An hana ma'aurata shiga kasar Amurka saboda mijin musulmine

Bayan sunyi aure kwananan, Ali Gul da amaryarshi natasha Politakis sun shirya zuwa kasar Amurka domin suyi irin holewarnan da akeyi ta bayan aure wato(HoneyMoon). Amma sun hadu da cikas a tashar jirgin sama inda suka sauka, domin kuwa bayan saukarsu daga jirgi sai jami'an tsaro suka killacesu domin yi musu tambayoyi.

Kamar yanda suka fadawa kafar yada labarai ta the sun, sunyi tsammanin abin bazai wuce na 'yan mintunaba amma sai gashi an kwace fasfonsu aka kuma amshi kayansu, saida suka kwashe awanni ashirin da shida sun tsare inda daga baya aka tasa keyarsu aka mayar dasu kasar Ingila inda suka fito.Ma'auratan sunce ba'a musu wani bayani ba dagane da irin wannan wulakanci da aka musu, amma dai kawai suna ganin cewa saboda shi mijin Natasha musulmine wanda dan asalin kasar Turkiyyane shiyasa aka hanasu shiga kasar ta Amurka.

Damadai Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana ta kokarin ganin ya hana baki, musamman musulmi shiga kasar ta Amurka, saidai wani jami'in ofishin jakadancin kasar Amurka ya bayyana cewa a kullun kasar Amurka tana amsar baki kusan miliyan daya, inda ya kara da cewa watakiladai akwai wani dalilin dayasa aka hanasu shiga ba wai dan addinin mijintaba.

No comments:

Post a Comment