Wednesday, 19 July 2017

An kama kasurgumar barauniya me shekaru tamanin da shida da satar gwal

Doris Payne 'yar shekaru tamanin da shida wata kasurgumar barauniyar gwalagwalaice wadda satarta bata tsaya a kasar Amurka inda aka haifeta kadaiba, harma wasu kasashe take ketarawa domin dai kawai ta saci sarka, dankunne, ko abin hannun gwal. Ta shafe shekaru 65 tana wannan harkar sata wadda takai har ana kiranda ta sunan me sana'ar sata.

Tana kyankyara kwalliyane Yanda idan ka ganta bazaka taba cewa bata da kudiba, sai ta shiga shagon sayar da gwalagwalai ta kira a kawomata kala-kalar gwal tana dubawa, a haka zataja me sayar da gwaldin da hira har ya manta yawan gwalagwalan daya kawomata sai ta shammaceshi ta dauki wanda take so ta fiyarta.

A tarihin sace-sacen da Doris tayi, an kamata da satar gwal har sau bakwai, akwai lokacin da tayi wata babbar sata wadda tafi kowacce na gwal wanda aka kimanta kudinshi yakai dalar amurka dubu dari biyar, kuma da aka kamata ba'a samu wannan gwal din ba, an sakata a gidan yari  amma ta shammaci ma'aikata ta tsere a lokacin wata dubiya da tajeyi asibiti.

Kai saboda tsabar addabar mutane da satar gwal da Doris tayi saida aka haramta mata shiga shagunan sayar da gwala-gwalai  kuma aka gayawa masu shagunan su saka ido karsu barta ta shigar musu shago.

Anyi kiyasin cewa Doris tayi amfani da sunayen karya akalla guda aahirin a rayuwarta, haka kuma tayi amfani da ranar haihuwa ta karya sau tara  da kuma wata lamba da ake cewa social security itama da dama.

A shekarar data gabata an kama Doris da laifin sata haka kuma shekaran jiyarnan, ranar Litinin an sake kamata da laifin wata satar gwaldin, inda ta shiga wani shago ta dauki kaya daban-daban ciki harda gwal, da taje biya sai bata biya kudin gwal din ba kawai ta sakashi a jakarta, ashe daya daga cikin masu lura da shagon y ganta, nan kuwa ya ankarar da jami'ai aka kamta.

Amma tace wani maganine datasha a gida kamin tazo shagon yasa take saurin manta abubuwa, bawai tayi niyyar yin sata bane, a lokacin wannan kamen nata na shekaran jiya an sameta da wani abin hannu wada akace shima ta sameshine daga satar da tayi ta karshe amin wannan.

No comments:

Post a Comment