Monday, 10 July 2017

An kirkiro wayar da bata amfani da batir

The Battery-free phone created by University of Washington researchers
Wasu kwararrun masu binciken kimiyya a jami'ar Washington dake kasar Amurka sunyi wata wayar salula wadda bata amfani da batiri, watakila wannan bajinta tasu ta faro asalin yin wayar da bata da batir, ganin cewa yanzu wayoyi da kwamfutoci dama kusan dukkan wasu kayan amfani na zamani, musamman na tafida gidanka zakaga suna bukatar batiri wanda daga lokaci zuwa lokaci yana bukatar a jonashi da wuta don yayi caji kuma idan yayi cajin karkari mutum yayi amfani dashi na tsawon kwana daya daga nan dole ka kara neman caja ka jonashi da wuta.

To idan wannan fasaha taci gaba wannan ba karamin sauki bane zai zowa al'ummar Duniya musamman mu 'yan Afrika ko ince Najeriya da wutar lantarki ta zamar mana matsala.

SHIN TA YAYA WANNAN WAYA KE AIKI?

Kamar yanda ake iya gani a wannan hoto na sama to haka wayar take, yanda take tana samun lantarki shine dolene a tsaya da ita a kewayen da wata na'ura take wadda daga itace wayar zata rika zuko wuta, watau misali ana iya cewa idan kana rike da wayar karkayi nesa da na'urar da take bata wutar na tsawon taku ashirin ko hamsin, ko kuwa ga misalin da kowa zai gane, kowadai yasan yanda ake amfani da Bluetooth wajen tura abu ko kuma WiFi wajan hada na'urar waya ko kwamfuta da yanar gizo, akwai nisan da zakayi bazaka samu wannan siginal din ba, to haka wannan na'ura takeba wayar lantarkin da take amfani dashi.

Ita kuma wayar tana amfanine da irin abinda rediyo ke amfani dashi wajen zuko magana tana samun lantarki daga waccan na'ura, kuma ayanzu dai kiran waya ne da amsa kiran kadai ake iyayi da wayar, bata da fuska bata da madannai irin wanda ka sani na waya haka kuma bazaka iyayin brauzin da itaba abinda kawai take dashi shine lambobi da za'a iya dannawa sai kuma wani madanni da idan za'ayi kira ko amsa kira ake amfani dashi.

Bazaka iya yin magana kamar yanda kakeyi da wayarka ta salula da wannan wayar ba, idan zakayi magana akwai madanni da zaka rike sai kafadi abinda kakeso wanda ya kiraka yaji sai idan ka saki wannan madannine sannan sakon zai jemai, haka shima idan zai mayarmaka da amsa zaiyi. haka kuma ana amfanine da sifikar kunne wajen sauraron sako daga wannan waya.

Ita wannan waya ba sunyita dan a sakata kasuwa bane a sayar, a'a sunyitane ta gwaji, sannan kamar yanda suka bayyana sunce suna saran wannan gwaji da sukayi zai bude idon sauran masu binciken fasaha a kirkiro wayar da za'a iya sayarwa mutane a kasuwa wadda bata amfani da batir kuma tana da dukkan abubuwan da wayoyinmu na zmani suke dasu.

Photo credit:University of Washington. 

No comments:

Post a Comment