Tuesday, 25 July 2017

An koyawa yara yanda ake aikin Hajji a aikace a kasar Malasiya

A jiya ne A kasar Malasiya aka shirya yiwa wasu yara dubu hudu 'yan shekaru shida koyarwar yanda ake aikin hajji a aikace, wadanda suka tsara abin sunja yaran zuwa bayan garin babban birnin kasar wato kuala lampor, suka yi daki me kama da ka'aba, da guri me kama da gurin jifar shedan, suka koyawa yaran yanda ake dawafi.

Duk da cewa an samu wadanda suka yaba da wannan abu da akayi amma mutane da dama sunyi Allah wadai dashi inda sukace be kamata ba bidi'ace wadda zata iya jawo fitina domin babu inda aka yadda ayi dawafi sai a garin makka, ka'aba.

Karin hotuna.

No comments:

Post a Comment