Thursday, 13 July 2017

An saka kudirin yiwa mazinata da masu yiwa mutane kazafi bulala a bainar jama'a cikin doka a kasar Malasiya


Jihar Kelantan dake kasar Malasiya ta saka yiwa mazinata da masu yiwa mutane kazafi bulala a bainar jama'a cikin doka, yan majalisar jiharne suka saka kudrin cikin doka a matsayin wani gyara ga tsarin shari'ar musulunci a jihar.

Shugaban 'yan majalisar jihar yace musulunci ya tanadi awa irin wadanda suka aikata wannan laifuka bulala a bainar jama'a domin ya zama darasi ga na baya, yace a yanzu da kudirin yin bulalar a bainar jama'a ya zama doka ya rage ga kotu ta bayar da damar yin bulalar a cikin mutane ko kuma a cikin gidan yari.A da dai kamin wannan doka ana yiwa wadanda bulala tahau kansu bulalarne a cikin gifan yari, kuma wanan kudiri na doka ya samu amincewar kungiyoyin addini daban-daban na jihar da kuma kungiyiyin mata masu fafutukar kare 'yanci musulmai.

No comments:

Post a Comment