Sunday, 30 July 2017

An yankemata hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari saboda yiwa bakar fata kazafi

Wannan yarinyar, ba amurkiya, farar fata ta gamu da fushin kotu, bayan tayi karyar cewa wasu bakaken fata guda uku sun saceta sannan suka yimata fyade.

Yarinyar 'yar shekaru sha tara da haihuwa, me suna Harmon, ta gayawa mahukunta a watan maris daya  gabata cewa wasu maza bakarfata su uku sun saceta suka kaita cikin daji,daya daga cikinsu ya riketa, biyu kuma suka mata fyade.

Amma da aka kaita gurin gwararrun likitoci sun bayyana cewa basuga wata alamar cewa an yimata fyade a jikinta ba, haka kuma akwai wani yanka a jikin wandonta wanda kwararru sukace baiyi daidai da yankan dake jikintaba, dadai yarinyar taga cewa karya ta kare, saita saduda ta gayawa kotu cewa dama can karyace ta shirya, hakan yasa kotu ta yankemata hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari.

No comments:

Post a Comment