Friday, 21 July 2017

An yiwa shugaba Buhari addu'o'in samun lafiya a kasashen Ingila da GiniAl'ummar Musulmin kasar Guinea Conakry sun yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari addu'o'in fatan samun sauki a masallatan Juma'an kasar.

A ranar Laraba ne Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya ba da umurnin gudanar da addu'o'in, a lokacin taron majalisar ministoci.

Shugaba Alpha Conde shi ne shugaban Tarayyar Afirka.Hakazalika, kungiyar Musulmin Najeriya a Birtaniya ta gudanar da addu'o'in rokon samun lafiyar Shugaba Buhari wanda yake jinya a Landan fiye da wata biyu a ke nan
.
A watan Maris da ya gabata ne aka tsara shugaba Buharin, zai kai ziyara Guinea, amma sai aka dage tafiyar tasa.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment