Tuesday, 11 July 2017

Anyi auren 'dan luwadi musulmi na farko a Duniya

An samu rahoton yin auren dan luwadi musulmi na farko a Duniya wanda ya fito bainar jama'a ya bayyana kanshi babu kunyar Allah balle ta mutane, Lamarin ya farune a kasar Ingila inda musulmin me suna Jahed Chodhury me shekaru 24 a Duniya ya auri masoyinshi, Sean Rogan dan shekaru 19.

Soyayyar tasu wadda ta samo asali shekaru biyu da suka gabata kamar yanda jahed ya bayar da labari, wata rana yana zaune yana kuka shi kadai sai ga Sean ya sameshi yake tambayarshi meke faruwa, da haka soyayyar tasu ko kuma muce tambadar tasu ta fara.Jahed yace ya samu kanshi a cikin wani mawuyacin hali bayan daya gano cewa shi dan luwadine kuma gashi musulmi, yace yayi kokarin ganin ya raba kanshi da wannan bakar al'ada ta hanyar zuwa aikin hajji ya roki Allah amma halayyar tashi bata canjaba, to daga nanne sai ya yarda da cewa haka rayuwarshi zata kasance kuma ya fito ya bayyanawa yan uwa da abikanshi irin halin dayake ciki.

Jahed yace fitowa fili da yayi yayi aure a matsayin dan luwadi zai kawowa kungiyar yan luwadi da madigo ta duniya cigaba yanda duk wanda ya tsinci kanshi a cikin irin wannan al'ada zai fito ya bayyanawa Duniya ba tare da jin tsoroba.

Haka kuma Jahed yace musulmai 'yan luwadi suma suyi amfani da wannnan fitowa da yayi ya bayyanawa Duniya halayyarsa a matsayin wata hanyar da zasu daina boye-boye, yace duk da cewa 'yan uwanshi basu halarci bikin auren nashiba saboda suna kallon abinda yayi a matsayin abin kunya to hakan bazaisa ya canja ra'ayiba.

Wannan dai yana batawa musulunci sunane kawai, idan me shiryuwane Allah ya shiryeshi. Amin.

No comments:

Post a Comment