Monday, 17 July 2017

Anyi bikin nuna kwalliyar akarnuka a Ingila

A jiya Lahadine akayi wani taron masu sha'awar karnukan pug a kasar Ingila, karnukan dai ba irin wadanda muke dasu bane anan, zaka gansu da tattararrar fuska da kuma gajeren hanci da idanu ciki-ciki amma manya. Haka kuma kananan karnukanne ake zuwa dasu irin wannnn biki banda manya. Taron anayinshine kamar biki yanda masu irin wadannan karnukan zasu yi musu kwalliya daban-daban su fito dasu zuwa gurin taron.
An shirya wasannin debe kewa kala-kala a gurin taron da kuma sayar da kayan ciye-ciye da tande-tande. Wani mutum me suna Martin ne ya shirya wannan bikin saboda tunawa da wani karen danshi daya taba bacewa aka ganoshi amma ya mutu

kuma masu irin wadannan karnuka sun bayar da hadin kai inda sukayita zuwa dasu suna zagayawa a gurin.

No comments:

Post a Comment