Tuesday, 18 July 2017

Ashe akwai wanda ya fi Dangote kudi a Najeriya?


Sanata Kabiru Marafa na Jam'iyyar APC da ke Wakiltar Jihar Zamfara a Majalisar Dattawa yayi da'awar kera mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote dukiya inda yace shi na shi mizanin awon daban.Babban Dan Majalisar yace a wajen sa shi wadatar zuciya ita ce arziki amma ba tsabar kudi ba. Sanatan yace idan kuma wannan ake magana to shi hamshakin attajiri ne don kuwa yana da wadata kwarai.Sanatan yace har yanzu hayan gida yake yi a Abuja kuma yace kashi sittin cikin dari na abin da ya samu hannun mutanen da su ka zabe sa yake komawa. Sanatan dai ya kara da cewa bai da handama ko kadan.
Naij.com

No comments:

Post a Comment