Monday, 17 July 2017

"Ba'a yabon dan kuturu sai ya shekara da yatsu": Anyi cece kuce akan wannan hoton na Hadiza Gabon da dan uwanta

Wannn hoton na jarumar fim din hausa, Hadiza Gabon da wani danuwanta data saka a shafinta na sada zumunta da muhawara ya jawo ce-ce-kuce sosai, A yayinda rubutun datayi a jikin hoton ya nuna cewa wannan dan uwantane na jini, wasu daga cikin mabiyanta sun nuna cewa hoton ya burgesu, wasu kuma suka fadi cewa gaskiya koda dan uwantane addinin musulunci lamunci su rika irin wannan kusansanceniyar da itaba.

Misali: daya daga cikin wadanda suka bayyana ra'ayoyin nasu yace " Ba'a yabon dan kuturu saiya shekara da yatsu, meyasa 'yan fim kukewa diokar Allah karan tsaye? Ke da muke ganin kinada mutunci, Ke kuma Hadiza yanzu wanan abu da kikayi menene marabarki da Rahama Sadau?"

Karin hotunan ra'ayoyin mutane akan wannan hoton.

No comments:

Post a Comment