Monday, 10 July 2017

Baturiya ta tofawa bakar fata musulma miyau a fuska

Labarin wannan baturiyar da hotonta ke sama ya karade shafukan zumunta da muhawara, bayanda aka ruwaito cewa ta tofawa wata mata bakar fata kuma musulma dake sanye da hijabi yawu a fuska haka kawai.
Wannan hoton musulmar da aka tofawa miyau a fuskarkenan
Abin ya farune a Can birnin Landan dake kasar Ingila, inda Wadda aka tofa mata yawun da abokinta suka saka wannan labari a dandalinsu na yanar gizo kuma sukayi kira da cewa Dan Allah a watsashi domin a samu yakai ga idon mahukunta, sunce kawai suna gefensu tsaye sai baturiyar tazo ta tofawa bakar fatar miyau a fuska sannan tace "mutane irinku".

Wasu dai sun yiwa wannan abu kallon nuna banbancin launin fata wasu kuma sunyimai fassara da cewa kin jinin addinin musuluncine saboda matar da aka tofawa miyan tana sanye da hijabi.

Wasu rahotanni da ba'a tabbatar dasuba sunce wannan mata 'yar Najeriyace.

No comments:

Post a Comment