Sunday, 16 July 2017

Buratai ya cika shekaru biyu a matsayin shugaban sojojin Najeriya

Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya cika shekaru biyu akan wannan mukami nashi da shugaban Kasa, Muhammadu Buhari  ya nadashi, nadin buratai a matsayin shugaban sojoji na daga daga cikin manyan nade-naden da shugaba Buhari yayi wanda ake yabawa.

A lokacin da aka bashi wannan mukami, Buratai ya gaji matsaloli da suka hada da rashin makamai in gantattu a hannun sojoji da matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso gabas na 'yan tada kayar bayar Boko Haram da kuma gazawa da sojoji suka fara nunawa, suna tserewa daga fagen daga saboda ba'a karfafamusu gwiwa yanda ya kamata.Amma cikin ikon Allah, hawan Buratai an samu canji, inda sojoji suka samu kayan aiki, Kwarin gwiwarsu ya karu, aka samu tsaro irin wanda aka jima ba'a samuba a yankin arewa maso gabas da kuma yankin Naija Delta Dama Najeriya baki daya.

Allah ya kara taimakon shi dama gwamnatin baba Buhari suci gaba da ayyukan alheri. Amin.

No comments:

Post a Comment