Friday, 28 July 2017

Dangote ya samu tawayar arziki, daga na hamsin da shida ya koma na dari da biyar

Hamshakin dan kasuwa kuma attajirin Duniya, Aliko Dangote ya samu nakasu a arzikinshi kamar yanda jaridar nan dake wallafa masu kudin Duniya ta Forbes ta bayyana, Dangote wanda a shekarar data gabata yana matsayi na hansin da shida, ya rikito kasan zuwa matsayina dari da biyar a cikin masu kudin Duniya.

Dalilin wannan fadowa ta Dangote yayi kamar yanda sabon rahoton jaridar na wannan shekarar ya bayyana, saboda karya darajar kudin nerane da gwamnatin Najeriya tayi, a yanzu dai Dangote yana da kudi dalar Amurka biliyan shabiyu da miliyan dubu dari biyu, wanda a shekarar data gabata, kudin Dangote sunkai dalar Amurka biliyan goma sha biyar da miliyan dubu dari hudu.A shekarar data gabata Dangote ya bayyana cewa yana so ya sayi club din kwallon kafar Arsenal nan da shekaru hudu masu zuwa, wannan abu daya fadi yasa kafafen watsa labari na Duniya suka mayar da hankali.kanshi sosai.


No comments:

Post a Comment