Saturday, 22 July 2017

Diyar sarkin musulmi, Fatima Sa'ad Abubakar ta kammala karatu daga wata jami'ar kasar Ingila

Diyar sarkin musulmi, Fatima Sa'ad Abubakar ta kammala karatunta na jami'a a wata makarantar dake kasar Ingila kwanannan, kuma mahaifinnata, sarkin musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar da sarkin kano Muhammad Sanusi na II sun halarci wajen bikin gama karatun nata.
Saidai wasu da sukayi sharhi akan hotunan da aka dauka sun bayyana cewa be kamata ace diyar sarkin musulmi a rika ganinta babu hijabiba. Munawa Fatima fatan Alheri, Allah yasa kuma karatun nata ya amfaneta da al'umma baki daya.

No comments:

Post a Comment