Monday, 10 July 2017

Diyar shugaban kasa Buhari, Zahara, ta bayyana halinda babanta yake ciki

Wani rubutu da diyar shugaban kasa, Zahara Buhari tayi akan dandalinta na Twitter dangane da rashin lafiyar babanta yaja hankulan jama'a sosai. Zahara ta gaishe da 'yan Najeriyane a shafin nata sai aka samu wani yayimata tambayar cewa "dan Allah ina mahaifinki yakene? Wannan tambayar na miki itane a madadin sauran al'ummar Najeriha"

Zahara ta amsamai da cewa yananan cikin hali me kyau(koshin lafiya),

Wannan yasa mutane da dama musamman masoya baba Buhari sukaji sanyi a ransu jin irin wannan magana ta fito daga bakin diyar cikinshi, sunsan cewa bazata fadi karyaba.

Saidai kafar yada labarannan dake bankado labaran sirri, wato Sahara Reporters ta wallafa wani.labarai dake cewa uwar gidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari data tafi Landan ganawa da me gidan nata bata samun ganinshi domin wasu 'yan neman suna da gindin zama sun hanata ganinshi, kuma wai shugaba Buharin na cikin wani mawuyacin hali .

Mudai munawa shugaba Buhari fatan Allah ya kaimai dauki ko a wane irin hali yake ciki kuma Allah ya dorashi kan makiya.Amin.

No comments:

Post a Comment