Saturday, 15 July 2017

"haba Maryam daga fara samun daukaka saiki rika yawo kai ba dankwali? kada ki zubar da mutuncinki"

Sabuwar jarumar fim din hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata kai babu dankwali, a hoton data saka wanda take sa hannu a lokacin da ta kulla yarjejeniya da kamfanin yin lemu na FruFru, wani yayi mata magana akan cewa, haba Maryam daga fara samun daukaka saiki fara yawo kai babu dankwali?"
To da alama maganar ta yiwa Maryam zafi, saboda data tashi saka wadannan hotunan nata wanda suma kannata babu dan kwali saita cire bayar da damar a bayyana ra'ayi a shafin ta na IG saboda kadama wani ya sake gayamata irin waccan maganar, Maryam tabi sahun Nafisa Abdullahine wadda itama tun da jimawa ta rufe bayar da damar a bayyana ra'ayoyi a dandalinta na shafin IG saboda bata jin dadin abinda ake gayamata.

To Maryam zata bar dandalin nata a haka babu ra'ayoyin mutane kokuwa zuwa nan gaba zata bayar da damar bayana ra'ayoyi? Lokacine kadai zai bayyana hakan, sai mu jira mu gani.

No comments:

Post a Comment