Wednesday, 12 July 2017

Hassan Giggs da matarshi Muhibbat Abdulsalam na murnar cika shekaru 9 dayin aure

Shahararren me bayar da umarni na finafinan hausa, Hassan Giggs da matarshi Muhibbat Abdulsalam suna murnar cika shekaru 9 dayin aure, Hassan ya bayar da labarin yanda ya hadu da matar tashi, yace wata ranane a shekarar 2005 a wajen daukar wani fim ya ganta ya mata magana amma bata amsashiba kawai tayi murmushi ta wuce, daganan kuma be kara ganintaba sai bayan shekara daya, daya ganta yace matata, wadda zan aura sai ta mayarmishi da amsa da cewa "a haka"?. Yace ya takaice zace dai yau gashi sunkai shekaru 9 dayin aure. Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara dankon soyayya ya kuma karawa wannan aure nasu albarka. Amin.

No comments:

Post a Comment