Sunday, 16 July 2017

Hoton shugaba Buhari dake yawo a shafukan sada zumunta ba sabo bane>>inji gwamnatin tarayya

Me baiwa shugaban kasa shawara kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad yayi magana akan hoton shugaban kasa, M. buhari da ma'aikacin gidan rediyon muryar Amurka ya saka a shafinshi wanda yake cewa sabon hotone. Bashir yace hoton ba sabobane an daukeshine tun watan fabrairun daya gabata lokacin da shugaba Buhari yaje Ingila karo na farko.

Hoton dai ya watsu sosai musamman a shafukan sada zumunta da muhawar kuma da dama sun amince dashi saboda ganin wanda ya saka hoton kwararren dan jaridane.

No comments:

Post a Comment