Wednesday, 26 July 2017

"Idan inada miliyan dari zan iya ba Hadiza Gabon miliyan casa'in da tara in rike miliyan daya"

Jarumar fim din hausa, me taimakawa yara, Hadiza Gabon ta saka wasu hotunanta da batayi irin kwalliyar zamani dinnanba a shafinta na sada zumunta da muhawara, kuma hotunan sunyi kyau sosai domin mutane da yawa sun yaba dasu.
A cikin wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu akan wadannan hotuna na Hadiza akwai ra'ayin wani bawan Allah daya ja hankulan mutane shima saboda abinda ya fada. Ga abinda yace kamar haka "wallahi idan inada miliyan dari zan iya baiwa Hadiza miliyan casa'in da tara in rike miliyan daya saboda irin soyayyar da nike mata"Wasu sunce fadar wannan magana kawai wannnn bawan Allah yayi wasu kuma sunce dan baiga miliyan darin bane, haka kuma wasu sunce babu abinda soyayya bata sawa.


No comments:

Post a Comment