Wednesday, 12 July 2017

"Ina harka da manyan mutanen kasarnan">>Ummi Zeezee

Jarumar fim din hausa, Ummi Zeezee ta saka hoton sahibinta(kamar yanda take kiranshi) wato tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi babangida inda yake tare da wasu kananan yara ta rubuta cewa yana son yara. Daya daga cikin mabiyanta ya amsamata da cewa lallai kinsan halin IBB domin kuwa tabbas yana son yara, mabiyin na Zeezee yacigaba da cewa abin na bashi mamaki yanda tasan halin IBB dama wasu manyan kasarnan haka.

Zeezee ta mayarmishi da amsar cewa ai tana harka da manyane shiyasa tasan halayensu.Gadai yanda hirar tasu ta kasance.

No comments:

Post a Comment