Friday, 14 July 2017

Irin wahalar da wannan yarinyar takeyi wajen debo ruwa zai baka tausai

Kamar yanda shafin yanar gizo na hukumar majalisar dinkin Duniya dake kula da harkar yara wato Unicef ya bayyana, wannan yarinyar Me suna Sulem, 'yar kasar Itofiyace, shekarunta 9, kuma wani abin tausayi dangane da rayuwarta shine tana zuwa debo ruwa daga gidansu zuwa gurin wani fanfan tuka-tuka, wanda tsawon tafiyar yakai kilomita tara.

Shafin ya kara da cewa, a kididdigarshi akwai mutane sama da biliyan biyu a Duniya da basu samun tsaftataccen ruwansha, haka kuma akwai mutane sama da biliyan hudu a Duniya da suke zaune a guraren da basu da tsafta.Shafin yayi kira da cewa ya kamata ayi kokari a dakatar da irin wannan matsalar, wadanda kuwa zasu taimaka wajen maganin wannan matsalar sune hamshakan attajiran Duniya, manyan gwamnatoci masu karfi da arziki, manyan kamfanoni na kasa da kasa.

Allah mun godemaka kuma muna yiwa wadanda ke cikin irin wannan hali, 'yan uwanmu, fatan Allah ya kaimusu dauki. Amin.

No comments:

Post a Comment