Saturday, 15 July 2017

Jadawalin kasashen dake samun yawan kiraye-kirayen wayar babu gaira babu dalili:Najeriyace ta tara

Kamfanin nan na manhajar True Caller, ya fitar da sunayen kasashen da sukafi samun yawan kiraye-kirayen wayar da babu gaira babu dalili, masu bata rai, wanda mutum be shiryamawaba a Duniya, Najeriyace ta tara a wannan jadawalin sunayen Kasashe, kuma kamar yanda kamfanin yace yawancin masu damun mutanen Najeriya da kiran wayar babu gaira babu dalili sune kamfanonin sadarwa kamarsu, MTN da Glo da Airtel da sauransu.
Kasar Indiyace ta farko a wannan jadawali sannan kasar Amerika da kasar Brazil da Chile da kasar Afrika ta kudu Mexico da Turkey da Peru sannan sai Najeriya.

No comments:

Post a Comment