Thursday, 27 July 2017

Jamila Nagudu ta fara samun sauki

Da alama jarumar fim din hausa, Jamila Umar, Nagudu ta fara samun sauki daga rashin lafiyar da tayi fama da ita wadda har takai ga ta kwanta a asibiti, an jima ba'aji duriyartaba a dandalinta na shafukan sada zumunta saboda rashin lafiyar, amma yanzu ta dawo da amfani da dandalin nata, wannan hoton na daya daga cikin wanda ta saka dake nuna alamar samun sauki tattare da ita.

Muna mata fatan Allah ya kara sauki, yasa kuma kaffarane. Amin

No comments:

Post a Comment