Friday, 14 July 2017

Kalli yanda aka kai wata amarya gidan mijinta da babur

Allah sarki rayuwa, kowa da daidai matsayinshi, idan ka kalli rayuwar wani sai kaga ka kara godewa Allah da matsayin da kake ciki, wannan hoton wani angone da amaryarshi Daya karade shafukan sada zumunta da muhawara, angon ya dauko amaryarshine akan babur suna rike daa lema, hakan da ba'a saba ganiba yasa wannan hoton ya dauki hankulan jama'a, wanda ya fara saka hotunan a shafinshi yace to 'yanmata masu korafin cewa saurayinsu bashi da mota ku kalli wannan hoton.

No comments:

Post a Comment