Wednesday, 26 July 2017

Kashi na Biyu:Abubuwan ban mamaki/birgewa wadanda gaskiyane/sun faru

Wannan rubutu kashi na biyune, wato cigaba akan na farko na abubuwan ban mamaki/birgewa wadanda gaskiyane/sun faru da shafin hutudole.com ya kawo muku, idan baka karanta kashi na dayaba to danna nan domin karantawa.

Kyautar shinkafa kwara goma kawai:

Akwai wani shafin yanargizo me suna freerice.com wanda zaka iya amfani da shafin ka bayar da kyautar kwayoyin shinkafa goma kacal: An bude shafinne domin mutane su taimaka wajen kawar da yunwa da wasu mutane ke fama da ita a Duniya, Wani mutum ne ya bude shafin, daga baya ya baiwa bangaren dake kula da abinci na majalisar din kin Duniya shi kyauta.

Yanda shafin ke aiki shine: zaka shiga shafin saika amsa wata tambaya da za'a maka, idan ka amsa tambayar daidai to wata talla zata bude, kudin wannan tallar daka gani sune za'ayi amfani dasu a siyi shinkafa a aikawa kasashen dake fama da Yunwa. Zaka iya cigaba da amsa tambayoyin iya iyawarka, a duk lokacin daka amsa tambaya daidai kamar ka sayi kwayoyin shinkafa gomane ka bayar kyauta. Shafin yace zuwa yanzu mutane sun bayar da kyautar kwayoyin shinkafa biliyan casa'ain da bakwai tun bayan kafashi.

Taurarin dake sararin samaniya sunfi yawan yashin da ake dashi a gabobin tekunan duniya yawa.

Cinnaku/tururuwa sunfi mutane yawa nesa ba kusaba, da za'a rabawa mutane cinnakun Duniya to kowane mutum daya zai samu cinnaka miliyan daya da dubu dari shida, haka kuma nauyin wadannan cinnaku kusan dayane da nauyin yawan mutanen Duniya.


A kasar China da kasar New Zealand akwai wasu gidajen namun daji(Zoo) wanda mutane ake sakawa a keji maimakon namun dajin: idan mutum yaje kallo za'a daukeshi cikin wata mota wadda bayanta wani kejine a kulle, a rika zagayawa dashi cikin gidan da namun dajin suke, su kuma namun dajin suna watayawa.

A kasar Ingila dokane mutum yayi fitsari akan titi ko kuma gurin da mutane ke taruwa, amma mace me ciki zata iyayin fitsari a duk inda take so, koda kuwa a cikin hular dan sanda tace tana so ya bata tayi fitsari, doka bata hanata ba.

A daa kwalar riga ba hade take da rigarba, ana iya cireta, kuma anyi hakanne saboda a samu saukin kudin wanki, saboda kwalar riga tafi ko ina wahalar wankewa.

Idan mutum ya dauki hoto tare da mutane yafi yin kyau fiye da ya dauka shi kadai: Wasu masu bincike na jami'ar California dake kasar Amurka sun bayyana cewa idan aka gabatar da fuskar mutum cikin jama'a tafi birgewa fiye da a gabatar da ita daya tilo.

Wannan hoton na kasa shine hoton farko da aka fara dauka a Duniya.
hoton farko da aka fara dauka a Duniya
National Geographic
Wannan hoton dake zuwa tare da mafi yawancin kwamfutocine(ada) rahotanni sukace anfi kallonshi fiye da kowane hoto a Duniya.
bliss windows photography facts
Microsoft
Mutumin da beyi yawo da yawaba a Duniya shine wanda yayi tafiyar datakai nisan zagaye Duniya sau uku kamin ya mutu. Wato mafi yawan mutane sunayin tafiyar data wuce zagaye Duniya sau uku a rayuwarsu kamin su mutu.

No comments:

Post a Comment