Sunday, 16 July 2017

Kedai ki dogara da Allah

Wasu matan sun samu mafi munin mutum, me sabon Allah(bama yiwa kowa fatan haka) a matsayin miji, kamar yanda Asiya ta auri fir'auna, amma hakan baisa ta canja kyawawan dabi'untaba da biyayya ga dokokin Allah ba.

Wasu kuma sun samu mafi kyawun halin mutane da biyayya ga Allah, kamar Annabawan Allah, amma duk da haka sun hallaka, misali matar Annabi Lut(A.S).

Wasu matan kuma basu samu yin aure ba kwatakwata a ruyuwarsu, kamar mahaifiyar Annabi Isa(A.S) wato Maryam(A.S) Amma kuma Allah ya daukakata fiye da kowace mace a Duniya.

Kedai ki dogara ga Allah ki kuma nemi taimakonshi a koda yaushe, Allah yasa mu dace. Amin.


No comments:

Post a Comment