Sunday, 30 July 2017

Kyan 'Da ya gaji Ubanshi:Ya kammala karatu da digiri me daraja ta daya daga wata jami'ar kasar Ingila inda babanshi yayi karatu

Wannan bawan Allahn da ake ganin hotonshi tare da iyayenshi, ya fito daga jihar Katsinane, karamar hukumar Daura, Mahaifar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sunanshi Abdullahi bukar, ya kammala karatunshi na Digiri daga jami'ar Swansea dake kasar Ingila a fannin Mechanical Engineering da digiri me daraja ta daya wato (first Class), Mahaifinshi shima wannan jami'a ya kammala a shekarar 1972. Muna taya Abdullahi murna da fatan Allah ya albarkaci wannan karatu nashi, yasa ya amfaneshi da dukkan al'umma baki daya.

karin hoto.

No comments:

Post a Comment