Sunday, 16 July 2017

Likafa tayi gaba: Zuwan MC Tagwaye da Morell kasar Canada

Shahararren me wasan barkwanci, MC Tagwaye tare da mawaki Morell kenan a lokacin da sukaje kasar Canada inda suka gudanar da tarukan nishadan tar da mutane a can. MC tagwaye yace ya hadu da wata yarinya wadda ita da mahaifanta sukazo Otal din daya sauka suka gaisheshi, yayi wani wani gajeren hoton bidiyo da yarinyar inda ya tambayeta daga ina take tacemai Najeriya ya kuma tambayeta me zata gayawa 'yan Najeriya tace "ku kyautatawa iyayenku".
Abin ya birge MC Tagwaye wanda har saida ya saka wannn sako a dandalinshi na shafin IG, inda yace to 'yan Najeriya kunji sakon da yarinyarnan ta aiko muku dashi.

A yanzu dai haka akwai wani taron wasan nishadin da MC tagwayen yake shirin yi a kasar Ingila, muna musu fatan alheri da da kuma Allah ya kara daukaka. Amin.

No comments:

Post a Comment