Tuesday, 11 July 2017

Majalisa tayi abin kai: An zartar da kudirin kula da wanda aka harba da bindiga a asibiti koda bashida kudi kuma koda babu dan sanda cikin doka

Majalisar dattijai tayi abin yabo bayan data zartar da kudirin dake bukatar idan an harbi mutum da bindiga aka kaishi asibiti a gaggauta kula dashi ba tare da an nemi sai yan sanda sunzo gurinba kokuma an samo rahoton yan sandaba cikin doka.

Majalisar wakilaice ta aikewa da majalisar dattijai da kudirin bayan ta kammala nata aikin kuma ayau 'yan majalisar dattijan sun saka wannan kudiri cikin doka. Dayake magana akan saka wannan kudiri cikin doka shugaba majalisar dattijai Bukola saraki yace ba kowane mutum da aka harba da bindiga bane mugu ko kuma me laifi, akwai mutanen da tsautsayi ko kuma wani ibtila'in yake fadamusu a harbesu da bindiga shiyasa saboda a rage yawan asarar rayukan da ake samu ta wannan bangaren muka zartar da wannan doka.Kudirin dai ya bukaci kowane mutum dansanda ko soja ko kuma farar hula ya baiwa duk wani wanda yagani da harbin bindiga taimakon dazai iya ba tare da wani bata lokaciba, haka kuma kowane asibiti, na kudi ko na gwamnati dolene ya amshi duk wani wanda aka kaishi an harbeahi da bindiga kuma abashi duk kulawar data kamata koda kuwa ba'a bayar dakosisiba.

Tabbas inda ace 'yan majalisa suna zartar da irin wadannan kudirori da zasu kawowa talaka saukin rayuwa cikin doka to da zagin da sukesha qajen talakawa ya ragu.

No comments:

Post a Comment