Monday, 10 July 2017

MANYAN NAMUN DAJI MASU TAUYE HAKKIN KANANAN DABBOBIN DAJI SUNA GAB DA KAUCEWA>>Inji Aisha Buhari

Image may contain: 1 person, closeup
A wani martani da uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ta maida wa Sanatan Kaduna ta Tsakiya Sanata Shehu Sani, inda yake bayyana "adduar kananan dabbobin daji (talakawan Nijeriya) ya ragu sosai ga Shugaban namun daji (Baba Buhari) inda manyan namun daji (Sauran masu rike da madafun iko a Nijeriya) suke cin karensu babu babbaka, suke ta shanawarsu a tunanin su shugaban ba zai dawo ba. Sai Aisha Buhari ta maida martanin cewa " Shugaban namun dajin (Baba Buhari) yana gab da dawowa, sauran kuraye da zakuna za su tattare kayansu su bar wurin, su kuma kananan namun daji ( za su cigaba da jin dadi).

Tabbas hakan yana nuni da cewa A'isha Buhari ta samu mijinta cikin sauki sosai. Wanda zai iya dawowa ba dadewa ba.


Allah ka dawo mana da shi lafiya.
rariya.

No comments:

Post a Comment