Saturday, 15 July 2017

Maryam Yahaya ta zama jakadiyar Lemun FruFru

Da alama sabuwar jarumar fim din hausa, Maryam Yahaya ta shigo masana'antar fina finan hausa da kafar dama, domin kuwa tun bayan fitowarta a fim din Mansoor wanda kamfanin babban jarumi Ali Nuhu ya shirya kuma fim din yake kan samun karbuwa a gurin 'yan kallo jarumar sai kara haskakawa takeyi, tun farko Ali ya bayyawa gidan rediyon bbchausa cewa baMaryamce yayi niyyar yin amfani da itaba a matsayin babbar jarumar fim din ba, amma dalilin rashin zuwan wadda yayi niyyar yin amfani da ita sai ya canja shawara yayi amfani da Maryam din.

To aikuwa wannan abu ba karamin alheri ya zamarwa Maryam ba domin a yanzu gashi kamfanin dake yin lemun FruFru ya mayar da ita jakadiyarshi, wato zata rika mai talla, saidai bamusan ko akan kudi naira nawa kamfanin ya kulla yarjejeniya da Maryamba.Muna mata murna da fatan Allah ya kara daukaka. Amin.

No comments:

Post a Comment