Sunday, 23 July 2017

Masu yada jita-jita sunji kunya:Kalli hoton shugaba, Buhari yana ganawa da jigogin APC a Landan

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorochas ya bayyana cewa sun gana da shugaban kasa, Muhamnadu Buhari a birnin landan fiye da awa daya, kuma ya bayyana shugaba Buhari da cewa akwai alamun kuzari a tattare dashi domin irin yanda aka sanshi da raharshi bai canjaba.

Ganawar wadda jigogin jam'iyyar APC sukayi.da shugaban.kasa, Buhari a landan ta samu halartar, gwamna Umar Tanko Almakura na Nasarawa, da Yahaya Bello na Kogi, da Malam Nasiru El-Rufa'i na Kaduna da kuma shugaban jam'iyyar APC wato Oyegun.

Rochas yaci gaba da aka tambayi shugaba Buhari akan irin labaran karya da wasu ke yadawa a gida Najeriya me zaice akan hakan?, sai yayi dariya, yace ba gaskiya bane, kuma yanawa 'yan Najeriya fatan alheri.

Haka kuma rahoton yace shugaba Buhari yana bibiyan duk wani abu dake faruwa a kasarnan, kuma nan bada dadewaba likitoci zasu sallameshi ya dawo gida Najeriya.

Okorocha yace masu yada jita-jita sunji kunya.

No comments:

Post a Comment