Tuesday, 25 July 2017

Mata sun nuna rashin jin dadi da ayyukan fyade

Dandazon matane suka fito a jihar Kano dan nuna rashin jin dadi da yanda ake samun yawan aikata fyade, sunyi kira da gwamnati ta rika hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki yanda ya kamata saboda ya zama darasi ga na baya.
Tsohuwar jarumar fim din hausa, Mansurah Isah matar babban jarumi kuma mawaki Sani Musa Danja, da diyarta Khadijatul Iman, sun shiga sahun wadanda ke nuna rashin jin dadi da yiwa mata fyade.

Saidai wasu sunyi kira da cewa  bawai fyade kawai ya kamata ayi kira da hanawaba, yin zina gaba daya ya kamata ayi kira da'a gujewa domin fitinace, da kuma saka kayan mutunci ga mata.

No comments:

Post a Comment