Thursday, 27 July 2017

Matan aure sun razana da yanda wannan budurwar ke kokarin kwacemusu mazaje

Wannan baiwar Allahn da ake ganin hotonta tana dariya a sama ta zamarwa wasu matan aure barazana, kamar yanda sakon da daya daga cikin matan auren ta aikamata ya nuna.

Baiwar Allahn me suna Habiba Manzo tace wata ta rubuto mata sako inda tace mata tasan tana da kyau, amma tana rokonta data daina saka hotunan ta a dandalinta na shafukan sada zumunta saboda tana jan hankalin mazajensu domin yanzu haka suna bibiyarta a dandalin da take saka hotunan, matar tace ba ita kadai take fama da wannan matsalarba akwai abokiyarta wadda itama mijinta na bibiyar Habiba saboda hotunanta suna birgeshi.Matar taci gaba da cewa shiyasa na yanke shawarar bari in miki magana/gargadeki, kije kiyi aure. Wannan sako yaba Habiba mamaki tace itada dandalinta?, wasu dai da sukayi sharhi akan wannan hoto sunyi kira da habiba datakai rahoto gurin 'yan sanda dan gudun abinda ka iya faruwa nan gaba.

No comments:

Post a Comment