Thursday, 27 July 2017

Matar data bude masallacin da mata da maza da 'yan luwadi ke sallah a sahu daya zata sake bude masallaci na biyu irinshi a kasar Ingila


Shedaniyar matarnan, 'yar kare hakkin mata(wajen ganin mata sun samu matsayi daya da maza a dukkan fannin rayuwa) me suna Seyran Ates, data bude masallacin data kira da baida kyamar kowa a kasar jamus, inda maza da mata da 'yan luwadi da madigo zasu iya haduwa a ciki suyi sallah a sahu daya(kafada da kafada), ta garzaya kasar Ingila inda tace acanma tanaso ta bude irin wannan masallaci.

Ta bayyanawa manema labarai cewa wannan abu da takeyi canjine da cigaba take so ta kawo a harkar addinin musulunci, matar 'yar asalin kasar Turkiyyace musulma kuma lauya amma yanzu tana zaune a kasar Jamus. Ta kara da cewa masallacin data bude a kasar jamus ya dauketa shekaru takwas tana ta shirye-shirye, amma wanda zata bude a kasar Ingila bazai dauki tsawon wannan lokaciba, tana sa ran nan da karshen shekararnan zai fara aiki, haka kuma tace bafa wai ita kadai take wanan aiki ba, akwai masu tallafa mata kamar su wata mata wadda take limanci a kasar Amurka, da wata mata wadda itama ta bude masallacin da mata kawai ke limanci a cikinshi da wani dan luwadi kuma limami wanda dan asalin kasar Algeriane amma yanzu yana zaune a kasar faransa, da kuma wani masanin harkokin addinin muslunci.A farkon bude masallacin kasar jamus datayi, Ates tace baza'abar duk wata me sanye da dankwali ko nikabi ta shiga masallacin ba, amma yanzu ta sassauta wannan doka inda tace idan mace tazo da hijabi ko nikabi to dole zata cireshi domin aga fuskarta, haka kuma za'a bata zabin ajiyeshi a gefe kamin tayi sallah.

Ates tace saka dankwali/nikabi ko hijabi wata hanyace kawai da maza suka bullo da ita wadda suke nuna cewa wannan (matar) tawace. ta kumace zasuyi kokarin ganin an bude musu kotu irin tasu ta musulmai masu baiwa kowa 'yanci a kasar Ingila, tundadai an yarda da bude kotun shari'ar musulinci.

Ates tace maganar shari'a kawai wata dabarace da wasu mutane ke fitowa da ita domin kokarin tauye hakkin mata, saboda haka su bazasu lamincetaba, haka kuma tace tana goyon bayan duk wata mace da batason saka hijabi/nikabi ko dan kwali dan ba dole bane.

No comments:

Post a Comment