Saturday, 15 July 2017

"Matata kyautace daga Allah a gareni">>Mukaddashin shugaban kasa, Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo ya saka sakon taya matarshi murnar zagayowar ranar haihuwarta, wanda ta cika shekaru hamsin a Duniya, a shafinshi na sada zumunta da muhawara, Sakon yaja hankulan mutane sosai kuma da yawa sun yiwa sakon daya fitar fassarar cewa lallai shi mutumne me so da kuma kulawa da matarshi daidai gwargwado, kuma akwai alamar kyakyawar fahimta a tsakaninsu.

Sakon nashi yace " Kyauta daga Allah, tana kula dani, tana bani goyon baya/taimakamin, tana tare dani, itace fukafukaina, wato matata kennan, ina tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki Oludolapo. Kece Muhimmin abinda nikeji dashi a rayuwata."

No comments:

Post a Comment