Sunday, 30 July 2017

MC Tagwaye ya tallafawa 'yan gudun hijira a jihar Katsina

Shahararren me wasan barkwancinnan, wanda ke kwaikwayar muryar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wato MC Tagwaye, ya kai taimako wasu matsugunan 'yan gudun hijira dake jihar Katsina, inda ya rabawa 'yan gudun hijirar kayan abinci da kudi, MC Tagwaye yace bawai sai mutum yana da miliyoyi ko kuma biliyoyin kudi ba sannan zai iya tallafawa wanda bashi da shiba, a'a ita sadaka bata kadan, kome kake ganin zaka iya tallafawa marar karfi dashi ya kamata kayi, muna fatan Allah ya bashi ladar yin hakan, ya kuma karomana irinshi a cikin al'umma. Amin.

karin hotuna.
No comments:

Post a Comment