Friday, 21 July 2017

Muhimmancin kyautatawa Iyaye, da kuma gujewa fifita mata akansu

A lokuta da dama akan samu 'yan mata dake son auren namiji wanda mahaifanshi, musamman mahaifiyarshi bata raye, waisu a ganinsu uwar miji tana ragewa rayuwar aure dadi, bazasu sakata su wala yanda sukeso ba. Amma fa karsu manta cewa ita wannan mahaifiya tana da wani hakki akanshi wanda saidai yayi iya yinshi amma bazai iya saukeshi gaba dayaba, kuma tun kamin kisan cewa zaki ganshi ko kuma yakai matsayin dayakai wanda har kike son aurenshi, ita wannan mahaifiya take tare dashi, kuma tamai dawainiyar da bazai iya biyandaba.

Nayi waccan matashiyane saboda labarai guda biyu dazan bayar wadanda suka shafi rayuwar aure da uwar miji, kamar yanda shirin jakar magori na gidan rediyon najeriya na Kaduna ya bayar. Labari na farko, wani bawan Allahne yaje neman auren wata mata, bayan sun daidaita suka amince zasuyi aure, sai tamai tambayar cewa kana da karnuka kuwa?Bawan Allahn nan ya mayarmata da amsar cewa shi baya kiwon kare a gidanshi tace to Alhamdulillah, akayi aure, kwana daya kwana biyu yaga matarshi bata kula da cewa a kaiwa iyayenshi abinciba, sai yaje yaje ya siyo kulan zuba abinci guda biyu yace to ga kwanukan iyayena, wannan na babane wannan kuma na mamane, idan anyi abinci a rika zubawa ana aikamusu dashi.

Budar bakin wannan mata sai tace, au ka manta da tambayar dana taba maka kamin muyi aure? Yace wace irin tambaya kenan? Tace mishi ka tunadai, can yadanyi nazari yace, au karnukan da kika tambayeni dama da iyayena kike?.

Baiyi wata-wataba ya saketa, dayake yana kishin iyayen nashi kuma yasan hakkinsu akanshi, to kajifa wai itama saikace bazata haifi da ba, zataso matar danta ta mata irin wannan cin fuska? Kuma daga ji itama batasan darajar nata iyayenba.

Labari na biyu, shima wani attajirine ya gina gida na gani na fada a birni, sai ya ware wani bangare ya gina daki da bayi, yaje kauye ya dauko Mahaifiyarshi ya sakata, kwana biyu sai matarshi ta kirashi ta gayamishi itafa ba zata iya zama da mahaifiyarshiba, saboda haka yazo ya dauketa, ba kunya ba tsoron ido, dayake ta shanyeshi, sai yazo ya dauke mahaifiyarshi ya mayar da ita kauye.

Ita kuma matar tashi da aka kwana biyu sai taje ta kawo mahaifiyarta gidan.

Wata rana rashin fahimta ya shiiga tsakanin wannan bawan Allah da matarshi, har yakai ga ya daketa, suna cikin kokawa, sai mahaifiyar matar tashi tazo gurin , a lokacin yana duke, sai ta dauko wani rodi da buga mishi a baya, nan kuwa ya kasa tashi, dalilin wannan cuta tashi saida kusan rabin kudinshi suka kare akan magani amm be samu lafiyaba.

To kaga wannan Allah ya nunamishi sakamakon abinda yayi tun daga Duniya, kamin su hadu. Allah shi kyauta ka hanamu yin aikin dqzai kaimu ya baromu.

No comments:

Post a Comment