Friday, 21 July 2017

Nawane karshen kirge?:Kasan sunan kudin dake gaba da trillion?

Idan akazo wajen kirgen kudi mutane da dama basu san wace kalma ake kiran karshen yawan kirge dashi ba, a hausadai wasu na cewa malala gashin tinkiya, wasu kuma idan sukaga abin ya wuce misali, sai suce ba iyaka, amma dai munsan komai nada iyaka banda ikon Allah.

To a kirgen turanci wanda mafi yawa dashi ake amfani, babban kirgen kudi yana farawane daga miliyan aje biliyan aje triliyan, wanda mafi yawan mutane basu san yanda ake kiran kudin dake gaba da triliyan ba.

Wasu na kiran kudin da ke gaba da trillion, wadanda zakai ta kara yawan sifili iya iyawarka da sunan Zillion, to amma a hukumance/ka'idar turanci ba'a yarda da wannan kalmarba.

To ga sunayen da ake kiran manyan kudi a harshen turanci wanda ya fara daga miliyan har zuwa karshe.

Million
Billion
Trillion
Quadrillion
Quintillion
Sextillion
SeptillionOctillion
Nonillion
Decillion
Undecillion
Duodecillion
Tredecillion
Quattuordecillion
Quindecillion
Sexdecillion
Septendecillion
Octodecillion
Novemdecillion
Vigintillion
Centillion.

A turancin kasar Amurka tun daga Million har zuwa Centillion za'ai ta kara yawan sifili ukune kawai.
Amma a turancin kasar Ingila, daga miliyan zuwa billion ne kawai ake kara sifili uku, idan za'a fara rubuta trillion har zuwa centillion banbancin yawan sifili shidane tsakaninsu.

kaga kenan a turancin kasar Amurka Centillion zai zama yana da sifillai dari uku da uku.

A turancin kasar Ingila kuma Centillion zai kasance yana da sifillai dari shida daidai.

Idan za'ai ta kara yawan sifillan sunan zai rika canjawane kawai da jimlolin llion a karshensu.

To amma akwai wasu kalmomi da aka samo daga wani yaro da aka taba tambayarshi cewa ya fadi sunan kudin da aka rubutasu da lamba daya da sifillai dari a bayanta, yaron yayi tunanin cewa dole wannan kudi sunada suna saboda baza'a iya kiransu da basu da iyakaba, sai yaron yace Googol, sannan kuma ya kara fadin wata kalmar wadda yace idan an rubuta lamba daya aka bita da sifillai iya iyawar mutum har ya gaji da rubutu to wannan za'a kirashi da Googolplex.

Wadannan sunye guda biyu wato Googol da Googolplex sune masu kamfanin yanar gizo na Google sukayi amfani dasu wajen sawa kamfanin suna da kuma shalkwatar kamfani itama me suna, Googleplex.

No comments:

Post a Comment