Monday, 10 July 2017

Rooney ya mika sakon Godiya/bankwana, me taba zuciya ga Manchester United

Tsohon dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya mika sakon godiya ga 'yan tsohon clubdin nasa bayan ya koma bugawa tsohuwar kungiyarshi wato Everton, ya fitar da sako kamar haka
"Ina mika godiya ta musamman ga masu gudanarwa na Club din manchester United da manajoji da ma'aikata da koci-koci danayi aiki karkashinsu da abokan wasana da muka buga ta mula tare da kuma musamman magoya baya dana bugawa wasa nagode da damar da aka bani"

Allah sarki akwai alamun kewa a wannan sakon daya fitar, koda yake shekaru 13 ba nan bane dole barin manchester United yaji ba dadi, amma dama komai yayi farko zaiyi karshe, Rooney dai yana da ragowar shekaru 3 nan gaba da zai buga wasan kwallo kamin yayi ritaya kamar yanda ya tsara, amma ata ukun watakila yayi wasa watakila kuma a cikinta zai daina doka wasa.

No comments:

Post a Comment