Monday, 31 July 2017

Sai kaso zaka zama mabaraci: Gaddafi me shan inna ya rungumi harkar noma

Wannan matashin, sunanshi Gaddafi kuma yana zaunene a jihar Zamfara, yana da nakasa a kafarshi baya iya amfani da ita, sanadiyyar cutar shan inna data sameshi tun yana dan karamin yaro, amma Gaddafi beje bakin titi ko bakin masallaci ba ya zauna yana neman baraba, ya rungumi harkar noma, anan gaddafine yake aikin cire ciyawa a gonarshi ta shinkafa, kuma yace yanzu beda budurwa amma yana fatan samun wadda zata zamar mai mata ta gari anan gaba. Munawa Gaddafi fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment