Saturday, 29 July 2017

Ta'addancin turawa akan bakakken fata lokacin mulkin mallaka:Rataye yarinya 'yar shekaru bakwai

A lokacin mulkin mallaka na turawa a kasashen Afrika, sun aikata abubuwan rashin imani kala-kala da sunan bautar da bakafata, saboda suna ganin cewa bakar fata ba cikakken mutum bane sannan kuma bashida basira da tunanin yanda ya kamata ayi rayuwar jin dadi.

A wannan hoton da kuke gani na sama wani ta'addancine da turawan kasar Belgiyom suka aikata a kasar Congo, wata yarinyace 'yar shekaru bakwai suka rataye saboda babanta ya kasa kawo yawan alkamar da suka bukaceshi da ita, kuma wai dan yaudarar kai, har saida suka karanta baibul kamin su rataye yarinyar.Tarihi ya nuna cewa an kashe mutane da dama a kasar ta Congo lokacin da turawan suke bautar dasu, a lokaci guda kuma suke tatsar arzikin kasar, amma mutuwar wannan yarinyar ya dau hankali sosai, masu tarihi da dama dai sun bayyana cewa akwai abubuwan da sukafi haka muni da turawa suka aikatawa bakar fata, amma kodai an lalata duk wani rubutu da zai bayyana hakan ko kuma an boyesu, kai wasuma abubuwan da suka faru ba'a dauki rahotanninsu ba.

No comments:

Post a Comment