Saturday, 29 July 2017

Tabewa: Musulmai masu neman mafakar zama a kasar Finland nata tururuwar komawa addinin kirista

Turvapaikanhakijat käyvät rippikoulua tulkin välityksellä.

Kafar yada labarai ta kasar Finland, YLE ta ruwaito labarin cewa musulmai da yawa da suka fito daga kasshen Afganistan, Iraki da Iran, suke kuma neman mafaka a kasar ta Finland, sunata tururuwar yin ridda zuwa addinin kiristanci.

Shugaban cocin dake jagorantar wannan aikin ridda yace suna samun daruruwan musulmai na zuwa domin yin ridda zuwa addinin kiristanci, shiyasa suka shirya wani shiri na musamman da zai ilimantar da sabbin shiga addinin na kiristanci yanda ake ayyukan addinin, yace sun rabawa wasu matsa da sukazo karbar addinin baibul, kuma wasunsu an musu wankan babtisma.


Faston ya kara da cewa yawancinsu masu neman mafakar zamane a cikin kasar Finland, Wani me suna Hussaini Aliraza yace"ba'a min wankan babtisma ba yanzu amma ina tsammanin kwanannan za'a yimin kuma nasan cewa zan zama kirista na gari".

Da yawan wadanda sukayi riddar sun bayyana cewa sunyi hakanne saboda rashin gamsuwa da addinin musuluncine da basuyi ba, da kuma alamun yaudara dake tattare da addinin, dukkansu sun tserene daga kasashensu na haihuwa kuma suna kan neman a basu mafakar zama a kasar ta Finland.

Haka kuma sun bayyana cewa a kasashensu na haihuwa ana nuna musu cewa su ba musulmai bane, kuma a halin yanzu basu da niyyar komawa kasashen nasu har abada,

Wani Hussaini Muhammad ya bayyana cewa" idan mutum ya koma addinin kiristanci zaifimai saukin samun zama a kasarnan saboda mafi yawancinsu kiristocine".

No comments:

Post a Comment