Friday, 28 July 2017

Tunatarwa akan abubuwan daya kamata musulmi yayi ranar Juma'a

Ranar Juma'a muhimmiyar ranace ga dukkan musulmin Duniya, akwai hadisi daga manzon Allah(S.A.W) wanda yake cewa: "Ranar Juma'ace tafi kowace rana a cikin ranekun mako, Ranar aka halicci annabi Adamu(A.S),  ranar ne annabi Adamu(A.S) ya shiga Aljannah, kuma a ranarne aka fitar dashi daga Aljannar, kuma a ranar Juma'ane za'ayi tashin kiyama(Muslim ya ruwaitoshi)".

Wasu daga cikin abubuwan daya kamata muyi ranar Juma'a sun hada da:

Yin waka:
Sahabin  manzon Allah, Abdullahi Bin Umar yace" Naji manzon Allah (S.A.W) yace" idan dayanku yayi niyyar zuwa Juma'a to yayi alwala". (Muslim ya ruwaitoshi)".

Saboda haka akwai bukatar mutum yayi wanka, ya tsarkake jikinshi da kyau ranar Juma'a.

Saka Tufafi masu kyau, yin asuwaki(brosh), Saka Turare.

Sahabin manzo Allah, Abu Sa'aid(R.A), yace naji manzon Allah(S.A.W) yace" yin wanka ranar Juma'a ga kowane musulmin daya kai shekarun balaga, wajibine, da kuma yin asuwaki da saka turare, idan akwai halin yin hakan"(Bukharine ya ruwaitoshi).

Saka tufafi masu kyau da tsarkake jiki yana da matukar muhimmanci a ranar juma'a, shiga masallaci da kaya me datti ko kuma jikin mutum na wari, zai iya cutar da sauran masallata, Allah ya bamu ikon yi.Tafiya Masallaci a tsanake:

Tafiya zuwa masallaci domin yin ibada ba karamin lada mutum ke samuba, Abu Huraira(R.A) yace yaji manzon Alla(S.A.W) yana cewa"Duk wanda ya tsarkake kanshi(yayi alwala)daga gidanshi sannan ya tafi zuwa daya daga cikin dakunan Allah(Masallaci) domin yin sallar farilla, to duk taku daya ana kankaremai zunubanshi sannan dayan takun ana daukaka darajarshi a gidan Aljannah"(Muslim ne ya ruwaitoshi).

Zuwa masallaci da wuri kamin liman ya fara huduba.

"A duk ranar Juma'a akwai Mala'ikun dake tsayawa a bakin Masallacin Juma'a suna daukar sunayen mutanen dake shiga Masallacin, mutum na farko daya fara zuwa zai samu lada kamar ya bayar da sadakar Rakumi, mutum na biyu daya shiga masallaci zai samu lada kamar ya bayar da sadakar Sa, mutum na uku zai samu lada kamar ya bayar da sadakar Kaza, mutum na karshe wanda zai samu karancin lada shine wanda zai samu kamar ya bayar da sadakar Kwai. Liman na fara Huduba Mala'ikun zasu rufe littafin daukar sunayen mutane suma su zauna su saurari Hudubar"(Bukhari da Musilimnne suka ruwaitoshi).

Yana da kyau mutum ya zauna kusa da Liman, yanda zai saurari Huduba da kyau.

"domin da liman ya fito yin Hudubar Juma'a Mala'iku suna zuwa susaurara(BuKhari ya ruwaitoshi).

Kada mutum yayi magana yayin da Liman yake Huduba ko kuma ya rinka soshe-soshen jiki ko kuma ya rika wasa da duwatsu, ana so mutum ya nutsu.

"duk wanda ya cewa abokin zamanshi kayi shiru, lokacin Liman ke Hudubar Juma'a to ya aikata abinki(Lagau)"(Bukhari da Musilim sun ruwaito wannan hadisi).

Yana da kyau mutum ya karanta suratul Kahf a wannan rana.

Yana da kyau mutum ya yawaita salati ga fiyayyen halitta(S.A.W) a wannan rana.

"A ranar Juma'a akwai wani karamin lokaci da idan mutum yayi dace dashi ya roki Allah wata bukata tashi, to Allah zai amsamai wannan addu'a"(Bukhari da Muslim sun ruwaito wannan Hadisi). Mafi yawan malamai sun bayar da karfi akan cewa wannan lokacin amsa addu'a yana tsakanin bayan sallar La'asar kamin ayi sallar Magariba. Allah yasa mu dace. Amin.No comments:

Post a Comment