Thursday, 13 July 2017

Wani mutum ya jira gwangwanin giya a matsayin kayanshi daga jirgi

Wani mutum a kasar Australia ya jira gwangwani daya tal na giya a matsayin kayanshi dake zuwa daga jirgi, ma'aikatan jirgin da sukaga wannan gwangwanin giya guda taya tal kuma da alamar shima kayane me zaman kanshi da wani ke jira ya amsa sunyi mamaki amma domin cika aiki sai suka makalamishi alamar da ake makalawa sauran kayan arziki,

Aikuwa da zuwan wannan gwangwani na giya sai jama'a suka cika da mamaki akaita kallo, sai kuwa ga wanda keda wannan gwangwani ya taso ya dauki abinshi, mutumin yace kaya da yawa sun iso amma bega gwangwanin giyarshiba , kadan ya rage yaje ya kai kara gurin ma'aikatan jirgin kan bacewar kayanshi dabai ganiba, "can kawai bayan duk na kosa sai naga mutane sunyi cin cirindo a gurin da kayan ke zuwa anata kallo, ina ganin haka saina tabbatar da cewa kayana ya iso" kamar yanda mutumin ya fada.Wasudai sun fassara wannan abu da cewa watakila kamfanin giyarne yake so ya tallata kanshi, wasu kuma wannan abin mamaki ya basu.


No comments:

Post a Comment